Giggs zai ci gaba da zama a United

Ryan Giggs
Image caption Ryan Giggs ya zira kwallaye 168 a wasanni 931.

Ryan Giggs ya sake sanya hannu kan kwantiragin shekara daya da Manchester United.

Dan wasan mai shekaru 39, zai ci gaba da zama a United har zuwa watan Juni na shekara ta 2014.

Wannan na nufin zai shafe shekara ta 23 tare da babbar kungiyar kulob din.

Tsohon kyaftin din na Wales Giggs ya fara taka leda a United a ranar 2 ga watan Maris na 1991 sannan ya zira kwallaye 168 a wasanni 931.

"Ina jin dadin zama da kwallon da nake bugawa fiye da kowanne lokaci, mafi muhimmanci shi ne ina jin dadin gudummawar da nake bayarwa ga kulob din," a cewar Giggs.

"Wannan babban kulob ne da ya kamata mutum yaji dadin kasancewa tare da shi, kuma gashi muna sake kokarin daukar kofuna a daidai lokacin da kakar ke karewa."

Karin bayani