Wilkins ya nemi Chelsea ta rike Lampard

frank lampard
Image caption Frank Lampard na cikin rashin tabbas a Chelsea

Tsohon mataimakain kociyan Chelsea Ray Wilkins ya bukaci kungiyar ta sabunta kwantiragin Frank Lampard .

Lampard mai shekaru 34 tun a shekara ta 2001 ya ke Chelsea amma kwantiraginsa ta yanzu za ta kare a karshen kakar wasannin da ake ciki.

A watan Yuni na 2001 Chelsea ta sayo Lampard daga West Ham a kan fam miliyan 11.

kuma ya ci wa klub din kwallaye 199 da su ka hada da 13 a bana a wasanni 593 da ya buga.

Sai dai kuma akwai rashin tabbas game da ci gaba da zamansa a kungiyar.

Ana rade radin cewa zai tafi Amerika ko China ko kuma Gabas ta tsakiya ya ci gaba da wasa.

A kan hakan Wilkins ya ke ganin hakan bata dace ba saboda Lampard din ya yi wa klub din kokari sosai a bana.

Kuma yana ganin zai ci gaba da hakan yadda ya ke da kuzari da sha'awar wasa.

Wilkins wanda ya buga wa Chelsea wasa sau 197 kuma shi ne mataimakin kociyanta a 200-10 lokacin da suka dauki kofin Premier da na FA ya bada misali da Ryan Giggs.

Ya ce Manchester United ta baiwa Ryan Giggs mai shekaru 39 karin kwantiragin shekara daya, saboda muhimmancinsa.

Karin bayani