Tottenham ta lallasa Arsenal

tottenham da arsenal
Image caption Tottenham ta ci Arsenal, ta zama ta uku a premier

A ci gaba da wasan Premier Tottenham ta samu nasara a kan Arsenal 2-1.

Gareth Bale ne ya fara jefa kwallo ragar bakin nasu a minti na 37 da fara wasa.

Minti biyu tsakani ne kuma sai Lennon ya kara ta biyu bayan da ya yanke mai tsaron gida da wata kwallo da aka sinna mishi tsakanin 'yan bayan Arsenal din.

Bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 51 Mertesacker ya rama wa Arsenal kwallo daya.

Da wannan nasara yanzu Tottenham ta maye gurbin na uku inda ta kawar da Chelsea da maki 54 yayin da Chelsea ta koma matsayi na hudu da maki 52 a wasanni 28.

Arsenal kuwa tana matsayi na biyar da maki 47, inda Manchester City ta ke ci gaba da kasance wa ta biyu da maki 56 amma wasanninta 27.

Manchester United ta ci gaba da bada rata a teburin da maki 71.