Ba tabbas kan gasar Kofin Duniya

tutar fifa
Image caption Gasar Kofin Duniya ta 2022 ka iya gamuwa da cikas

Da alamu za a daga lokacin gasar cin Kofin Duniya na kwallon kafa ta 2022 a Qatar.

Hakan na iya kasance wa ne kuwa idan binciken masana harkokin lafiya ya tabbatar cewa yanayin zafi a lokacin na da hadari.

Wani babban jami'in Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ne ya tabbatar da hakan.

Ya ce idan aka tabbatar yanayin zafi a Qatar a wannan lokaci na bazara zai yi tsananin gaske za a daga lokacin gasar.

Sa dai FIFA ta ce za a daga lokacin ne idan hukumomin kasar suka bukaci hakan.

Tun kafin yanzu shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai Michel Platini ya goyi bayan shawarar dage gasar daga lokacin da aka saba fara gudanar da ita na watan Yuni.

A wannan lokaci a Gabas ta Tsakiya zafi yakan kai maki 50 a ma'aunin Celcius.

Domin kawar da fargaba game da lamarin hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawan su ma sun ce sun yi niyyar amfani da filayen wasa masu na'urorin sanyaya wuri.

kuma su na bincike kan yuwuwar kirkirar hadari don sanyaya yanayi a lokutan wasannin.