Sai Arsenal ta yi da gaske - Wenger

Manajan kulob in Arsenal, Arsene Wenger
Image caption Arsene Wenger ya ce za ta yi kokarin shiga gasar champions league, duk da cewa za su kara da Manchester City da kuma Liverpool

Manajan kulob din Arsenal, Arsene Wenger yace sai kulob din ya yi da gaske, kafin ya shiga jerin kulob hudu na gasar premier.

Ya bayyana hakan ne bayan kulob din Tottenham ya doke Arsenal da ci biyu da daya.

Arsenal dai na da maki bakwai, a bayan Spurs wanda kulob na uku ne a gasar, yayin da Chelsea kuma ita ce ta hudu kuma tana gaba da Arsenal da maki goma.

"Lallai sai mun yi da gaske, kuma a yanzu kamar wuri ya kure mana, saboda mun rasa wasu maki da bai kamata ace mun rasa su ba. " A cewar Bafaranshen.

Ya kara da cewa "Amma za mu zage damtse, kuma ba za mu karaya ba."

Tun shekarar 1995 kawo yanzu Arsenal ta kasa shan gaban Spurs, haka kuma ta kasa shiga cikin jerin kulob-kulob hudu na gasar premier tun a shekarar 1996, da ta zo ta biyar.

A halin yanzu kulob din na cikin shekara na 15, yana wasa a gasar champions league.