An dakatar na Bendtner watanni 6

nicklas bendtner
Image caption Nicklas Bendtner ba zai samu gayyatar Denmark ba

Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Denmark ta dakatar da dan wasan kasar Nicklas Bendtner tsawon watanni shida bayan da aka kama shi da laifin tukin mota cikin maye.

Dan wasan gaban mai shekaru 25 wanda Arsenal ta baiwa Juventus aronsa a bana tun watan Disamba ba ya wasa saboda raunin da ya ji.

Aranar Lahadi ne aka kama shi yana tuka mota a titin da bai dace ya bi ba a Copenhagen.

A sakon da ya aike ta shafin Internet na Twitter ya ce ''ina neman gafara daga dukkanin abokanaina da masu sha'awar wasana.''

''Tuki cikin maye abu ne da bai dace ba. Na dauki alhakin duk abin da ya faru.''

Hukumar Kwallon Kafar ta Denmark ta ce za a tuhumi dan wasan da laifin saba dokar tuki kuma sabo da haka ba za a gayyace shi buga wa kasar wani wasa ba.

Dangane da hakan Brendtner ba zai buga wasannin neman zuwa gasar cin Kofin Duniya na 2014 da Denmark za ta yi da Jamhuriyar Czech da kuma Bulgaria nan gaba a wannan watan ba.