Kocin Bulgaria na yajin cin abinci

bulgaria wrestlers
Image caption Wasan kokawa shi ne Bulgaria ta fi nasara a kai

Kocin wasan kokawar wrestling na kasar Bulgaria ya shiga yajin cin abinci domin nuna korafinsa akan matakin fitar da wasan kokawar daga jerin wasannin Olympics daga shekara ta 2020.

Hukumar kula da kokawar ta Bulgaria ta ce kocin mai suna Armen Nazaryan ba zai ci abinci ba daga yanzu har sai an kai lokacin fara gasar kokawa ta kasashen Turai ranar 22 ga watan Maris zai rinka shan ruwan 'ya'yan ita ce ne kawai a tsawon wannan lokaci.

Kocin haifaffen kasar Armenia sau biyu yana samun lambar yabo ta zinariya a wasannin olympics na 1996 da 2000.

Wasan kokawa dai shi ne Bulgaria ta fi fice a kansa a gasar Olympics inda ta ke da lambobin zinariya 16.

A watan da ya gabata ne Hukumar Wasannin Olympics ta Duniya ta kawo wannan shawara ta bazatta cewa za a cire wasan na kokawar na tun tale-tale daga gasar Olympics a 2020.

Wannan mataki dai ya jawo cece-kuce daga masu sha'awar wasan a duniya har ta kai wasu tsoffin zakarun wasan na Olympics Valentin Yordanov da Sagid Murtazaliev na Rasha su ka maida lambobinsu na yabo na gasar ga Hukumar olympics din ta duniya.

Karin bayani