Ferguson : Ba ma tsoron Ronaldo

alex ferguson
Image caption Alex Ferguson ya ce Ronaldo ne babbar barazanar Man United

Yayin da ake shrin karawa ta biyu tsakanin Manchester United da Real Madrid a gasar Zakarun Turai ranar Talatar nan kocin United Sir Alex Ferguson ya ce ba za su ji tsoron Ronaldo ba.

Kociyan ya kafe cewa Manchester United ba za ta ji tsoron Cristiano Ronaldo ba a karawar tasu a Old Trafford duk da cewa shi ya ci United din a karawar farko a Bernabeu da suka tashi 1-1.

Ferguson ya ce ''ba abu ne da zai tada mana hankali ba.

Idan muka damu da ta'annatin da zai iya mana to kuwa zamu manta da abin da zamu iya yi.''

Amma kuma duk da karfin halin na Ferguson ya lamunta cewa dan wasan da ya rena a Old Trafford kafin Real Madrid ta saye shi a kan fam miliyan 80 a 2009 zai iya zamar musu babbar barazana ga fatansu na zuwa wasan gab da na kusa da karshe na Zakarun Turan.

Sir Alex ya ce '' to me kake tsammani idan kana wasa da kungiyar da take da Ronaldo a cikinta?

Ba shakka dole ne ka yi tsammanin matsaloli a lokacin wasan amma za mu yi duk abin da zamu iya mu hana hakan.''

A shekara ta 2003 takwaran Cristiano Ronaldon wato Ronaldo na Brazil ya ci Manchester United kwallaye uku rigis a Old Trafford da suka yi waje da United din a wasan gab da na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai a karawarta da Real Madrid din.

Karin bayani