Man City ta kara kusantar United

aston villa da manchester city
Image caption Manchester City ta kara matsawa a Premier

Manchester City ta kara rage ratar da ke tsakaninta da Manchester United ta daya a gasar Premier zuwa maki 12.

Manchester City ta na jagba ne a gasar ta Premier da maki 71 a wasanni 28.

Man City ta biyu a tebur ta samu wannan nasara ce bayan da ta yi galaba a kan Aston Villa wadda ke wasa a gida da ci 1-0.

Carlos Tevez ne ya ci kwallon daya tilo ana gab da tafiya hutun rabin lokaci a minti na 45.

Aston Villa ta ci gaba da kasance wa cikin kungiyoyi uku da ke cikin hadarin faduwa daga gasar Premier inda ta ke matsayi na 18 da maki 24 a jerin kungiyoyi 20.