Jinkiri game da komawar Martins Amurka

Obafemi Martins
Image caption Obafemi Martins ya yi fama da rauni a kulob din Rubin Kazan

An samu jinkiri game da komawar Obafemi Martins gasar Major League Soccer ta Amurka, inda a yanzu ba a saran kammala yarjejeniyar har sai akalla mako mai zuwa.

Da farko an zaci cewa dan wasan na Najeriya zai kammala shirinsa na komawa MLS daga Levante ranar Asabar bayan da ya amince da yarjejeniyar a farkon makon nan.

An tsara Martins zai tashi zuwa Amurka ranar Juma'a sai dai an sanya shi a tawagar Levante a fafatawar da suka yi da Valencia ranar Asabar.

Tsohon dan wasan na Newcastle da Birmingham City ya bayyana cewa an jirkinta batun tafiyar.

"Akwai dan jinkiri amma ina da kwarin gwiwar cewa komai zai daidaita," Martins ya shaida wa BBC Sport.

"Dan sabanin fahimta aka samu. Amma za mu shawo kan lamarin."

Dan wasan Najeriyar ya koma Lavante bayan da ya kasa kai bantansa a Rubin Kazan na Rasha, inda ya rinka fama da rauni da rashin kokari, abinda ya sa suka rinka zaunar da shi a benci.