Man U za ta kara da Real Madrid

Sir Alex Ferguson da Jose Mourinho
Image caption Sir Alex Ferguson da Jose Mourinho

Mai horar da 'yan wasan kulob din Real Madrid, Jose Mourinho ya ce " Duniya za ta tsaya cik domin kallon karon batta tsakaninmu da Manchester United" a ranar Talata.

Kulob din biyu dai kowannensu ya daura damara, bayan kowannensu ya samu galaba da ci daya a kan abokan karawarsu, a zagayen farko a Bernabeu.

Manajan Real kuma yayi amanna cewa wasan zai ja hankali sosai.

"Babu wanda zai iya cewa ga abin da zai faru, saboda kar ta san kar ce." Inji Mourinho.

Real ta isa filin wasa na Old Trafford, bayan ta samu nasara sau biyu a kan Bercelona a 'El-Classico'.

Real ta doke Berca ne da ci uku da daya a zagaye na kusa da na karshe, a gasar cin kofin Del Rey, kuma ta sake lallasa ta da ci biyu da daya a gasar La Liga.

Ita ma Man U za ta shiga karawar da kyakkyawan shiri, domin ba a taba doke ta ba a wasanni biyar da ta buga a gasar, kuma ga ta yanzu a zagayen gaf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin FA, bayan ta doke Reading da ci biyu da daya.