Golf : Rory Mcllroy ya yi nadama

rory mcllroy
Image caption Rory Mcllroy na fuskantar koma baya a wasansa

Zakaran kwallon Golf na duniya Rory Mcllroy ya yi nadamar ficewa daga fili da ya yi a gasar Honda Classic.

Zakaran kwallon lambun ya fice daga gasar a Florida ta Amurka a zagaye na biyu a makon da ya gabata.

Daga bisani ya ce ya yi hakan ne saboda ciwon hakori mai tsanani da ya taso masa a lokacin.

Sai dai kuma Mcllroy yanzu ya yi nadamar yanke wannan shawara ta barin wasan, ya ce, ''hakan ba abu ne mai kyau ba ga wasan da kuma yara da 'yan kallon da suka taru suna kallo na.''

''Abin da ya kamata na yi shi ne na daure na ci gaba.''

Shi dai Mcllroy tun a farkon shekarar nan da ya rinka sauya kungiya ya ke fama wajen gano bakin zaren bajintarsa a wasan na golf.

Zakaran ya kuma kara jaddada matsayinsa kan wannan matsala cewa shi fa ba ya dora alhakin koma bayan nasa a kan kayan wasansa.

Ya ce yana dai bukatar kara zage damtse ne kamar mutumin da ya kawar a matsayi na daya, wanda ya dade yana zaman lamba daya a fagen wasan na Golf wato Tiger Woods.