Kofin Zakarun Turai ne Burin Chelsea

chelsea
Image caption Chelsea na fafutukar zuwa gasar Zakarun Turai

Shugaban Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Ron Gourlay ya ce yana daga burin klub din a yanzu ya samu damar zuwa gasar Kofin Zakarun Turai mai zuwa.

Klub din ne dai ya dauki Kofin a kakar wasanni ta 2011-12 amma kuma aka fitar da shi a matakin wasan rukuni a wannan karon kuma ya na matsayi na 4 a Premier yanzu.

A matakin da ya ke yanzu na hudu a gasar ta Premier zai samu damar zuwa gasar ta Zakarun Turai amma idan ya yi kasa da haka ba zai samu dama ba.

Maki biyu ne yanzu tsakanin Chelsea da Tottenham wanda ke matsayi na uku a Premier kuma maki biyar tsakaninsa da Arsenal dake matsayi na biyar.

Gourlay ya ce samun gurbi daya daga cikin hudu na kungiyoyin da ke gasar Premier wadanda za su je gasar ta Kofin Zakarun Turai yana daga burin Chelsea.

Gourlay ya ce suna son ganin klub din nasu ya fafata da manyan klub klub na Turai a kakar wasanni ta gaba.