Kofin FA : Man United da Chelsea

ryan giggs
Image caption Ryan Giggs zai huta a wasan Man United da Chelsea

Ana saran Ryan Giggs ba zai buga wasan gab da na kusa da karshe na kofin kalubale na FA ba tsakanin Manchester United da Chelsea saboda zai huta.

Za a sa Antonio Valencia ko Ashley Young a madadinsa, yayin da Phil Jones da Paul Scholes su ma dukkanninsu ba za su yi wasa ba saboda rauni.

A bangaren Chelsea kuma Demba Ba da Victor Moses da Ramires da Nathan ana saran za su yi wasa.

'yan wasan na Chelsea ba su sami damar buga wasan kungiyar na kofin Europa ba da Steaua Buchuresti ta yi nasara a kanta ba.

Sau 165 manyan kungiyoyin na Premier suka hadu, Manchester United ta yi nasara sau 72 ita kuma chelsea ta sami galaba a kan United sau 45 suka tashi canjaras sau 48.

Karin bayani