Ferguson ya ki gaisawa da Benitez

Alex Ferguson da Benitez
Image caption Alex Ferguson da Benitez

Mai horar da 'yan wasa na rikon kwarya na kulob din Chelsea, Rafeal Benitez ya ce manajan Manchester United Sir, Alex Ferguson ya ki yarda su sha hannu, gabbanin karawarsu ta ranar Lahadi.

Mutanen biyu dai ba su da kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu, kuma yanzu hakan ya sake kunno kai a filin wasa na Old Trafford.

"Da fari na jira shi, kuma na san mutane da dama na kallo yadda za mu yi, saboda haka na san abin da zan yi." Inji Benitez

Ya kara da cewa" Ya rage na shi domin na tsaya a kan hanyar fitowarsa, ina jiransa, ku tambaye shi ku ji."

Dangantaka ta fara tsami ne a tsakaninsu a shekarar 2009, a lokacin da Benitez na manajan Liverpool ya yi ikirarin cewa, hukumar kwallon kafa ta Ingila ta fi nuna fifiko ga dan yankin Scotland wato Ferguson.

Haka kuma bayan an hura usur na kammala wasan da kulon din suka buga a ranar Lahadi, Ferguson da Banitez sun ki gaisawa da juna.

Chelsea ce dai ta doke Manchester da ci daya da nema, a wasan gaf da na kusa na karshe a gasar cin kofin FA.