Zakarun Turai : Barcelona ta tsallake

lionel messi
Image caption Lionel Messi ya ceto Barcelona

Barcelona ta tsallake zuwa wasan gab da na kusa da karshe na cin kofin Zakarun Turai bayan da ta lallasa AC Milan a Nou Camp da ci 4-0.

A karawarsu ta farko AC Milan a gidanta ta ci Barcelona 2-0, da wannan sakamakon na biyu jumulla Barcelona ta na da kwallo 4 Milan ta na da 2.

A wasan na biyu Messi ne ya fara cin kwallo a minti 5 da wasa, sannan kuma ya kara ta biyu a minti na 40.

Bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci ne kuma David Villa ya ci ta uku.

Jordi Alba ne kuma ya kammala ta hudun bayan cikar minti 90 ana shirin tashi daga wasa.

Barcelona ta kafa tarihi a gasar kofin Zakarun Turan da ta zama kungiya ta farko da aka ci a karawar farko a waje ta zo gida ta rama har ta wuce gaba.

Karin bayani