'Yan wasan da suka fi kudi a duniya

tiger woods
Image caption Tiger Woods ya fi David Beckam kudi

Duk da tsabar dukiyar da suke da ita ta fam biliyan 1.7 'yan wasan kwallon kafar nan 50 da suka fi kudi a duniya ba su kama kafar takwarorinsu na wasan kwallon kwando da tennis da golf da kwallon zari ruga ta Amurka ba.

David Beckam wanda ya zama na daya a jerin 'yan kwallon kafa 50 da suka fi kudi a duniya da fam miliyan 172 ko alama bai kusa da irin su tsohon zakaran wasan golf Tiger Woods da tsohon zakaran tseren mota Micheal Schumacher ba.

Tiger Woods wanda yanzu ke kan hanyarsa ta sake komawa na daya a wasan golf an yi kiyasin ya na da zunzurutun kudi fam miliyan 538, ya yin da shi kuma Schumacher ya ke da fam miliyan 510.

Sai dai kuma wasu fitattun masana a harkokin wasanni na ganin Messi da Ronaldo wadanda suka ce ba a biyan su kudade yadda ya kamata ka iya zarta duk wani dan wasa kudi idan suka yi amfani da damarsu sosai.

Saboda 'yan wasan sun yi suna a kowana sako da lungu na duniya.

Karin bayani