Zakarun Turai : Galatasaray ta yi nasara

galatasaray da schalke
Image caption Galatasray ta casa Schalke 04 ta tsallake gaba a gasar Kofin Zakarun Turai

Kungiyar Galatasaray ta samu nasarar zuwa wasan gab da na kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai inda ta yi nasara a kan Schalke 04 da ci 3-2 a Jamus.

A karawarsu ta fako a Turkiyya gidan Galatasaray sun tashi kunnen doki 1-1.

Sakamakon karawar biyu ya kasance Galatasaray na da ci 4 Shalke 04 ta na da ci 3.

Neustadter na Shalke ne ya fara cin kwallo a minti na 17 kafin Altintop ya rama wa Galatasaray a minti na 37.

A minti na 42 kuma sai Yilmaz ya ci wa Galatasaray kwallonta ta 2 amma kuma Michel Bastos ya rawa aka zama 2-2 a minti na 63.

Glatasaray ta samu kwallonta ta uku ne a minti na 90 ta hannun Bulut.