'Yan bindiga sun jikkata malamai a Kano

Taswirar jihar Kano dake arewacin Najeriya
Image caption Duk da cewa gwamnatin jihar Kano ta hana hawa babur mutum biyu, har yanzu ana amfani da babura wajen kai hari

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun bude wuta a kan wasu malaman makarantar firamare a jihar Kano, inda suka jikkata hudu daga cikinsu.

Cikin wadanda ke samun kulawa a asibiti a sanadiyar harin har da shugaban makarantar.

Lamarin dai ya faru ne da safiyar ranar Talata a makarantar firamare dake Unguwar Dan Maliki da ke tsakanin unguwar Sabuwar Gandu da kuma garin Kumbotso.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da lamarin.

'Yan bindigan su biyu fara tambayar Malaman, domin sanin ko a cikinsu akwai wanda baya koyarwa, kafin su bude musu wuta su hau kan babur su tsere.