Wilshere zai yi jinyar mako uku

Jack Wilshere
Image caption Wilshere bai samu shiga kakar wasannin bara ba saboda karayar da ya samu a agara

Dan wasan tsakiya na kulob din Arsenal, Jack Wilshere ba zai buga wasanni ba a tsawon makonni uku masu zuwa, saboda raunin da ya samu a agara.

Hakan kuma ya sa ba zai samu shiga wasan share fagen, cin kofin duniya na Ingila ba.

Abin da ke nufin dan wasan mai shekaru 21 ba zai buga wasan share fagen da kulob dinsa zai yi da San Marino da Montenegro a watan Maris da muke ciki ba.

Haka kuma ba zai shiga takaleda tsakanin Arsenal din ba da Bayern Munich, wanda za a yi a ranar Laraba.

Wilshere ya samu raunin ne a fafatwar da suka yi a Tottenham, inda Asernal ta lallasa abokiyar karawar tata da ci 2-1, a ranar 3 ga watan Maris din da muke ciki.

Duk da cewa wasa bakwai kawai ya buga, ana kallon Wilshere a matsayin dan wasan tsakiya da Roy Hodgson ke son ya sanya a cikin 'yan wasan Ingila.

Kasar dai na neman shiga zagayen karshe a gasar cin kofin kwallo na duniya ta shekarar 2014.