Zakarun Turai : An yi waje da Arsenal

bayern munich
Image caption Bayern Munich ta yi waje da Arsenal

Bayern Munich ta fitar da Arsenal daga gasar cin Kofin Zakarun Turai na kwallon kafa.

A wasan da suka yi a Munich ta Jamus Arsenal ta ci Bayern 2-0 amma kasancewar a karawarsu ta farko a gidan Arsenal an ci Arsenal din 3-1 sakamako ya kasance 3-3.

Hakan ya sa Bayern ta yi galaba saboda kwallayen da ta jefa wa Arsenal a gida.

A wasan nasu na ranar Laraba Giroud ne ya fara ci wa Arsenal kwallo a minti uku da wasa.

Can a minti na 86 ne kuma Koscienlny ya kara ta biyu.

Da wannan sakamako da ya kawo karshen fatan Arsenal na daukar wani kofi a bana yanzu ya kasance shekaru takwas ke nan ba ta dauki kofi ba.

Kuma wannan shi ne karon farko a shekaru 17 da ba bu wata kungiyar kasar Birtaniya a wasan gab da na kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai.

Malaga da FC Porto

Malaga ta tsallake zuwa wasan gab da na kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai bayan ta ci FC Porto 2-0 a gidanta Spain.

Malagan ta samu wannan dama ce bayan da a wasansu na farko a gidan FC Porto (Portugal), 'yan Porton suka yi nasara a kanta 1-0.

Wannan shi ne karon farko a tarihin klub din na Malaga da ya kai wasan gab da na kusa da karshe na kofin na Zakarun Turai.