Ghana ta gayyaci Frimpong

emmanuel frimpong
Image caption Burin Emmanuel Frimpong ya cika na yi wa Ghana wasa

Hukumar kwallon kafa ta Ghana ta gayyaci Emmanuel Frimpong domin ya fara buga wa kasar wasa.

Dan wasan mai shekaru 21 dan Arsenal ne amma yana zaman aro a Fulham yanzu.

Frimpong wanda haifaffen Ghana ne amma ya tashi a Ingila ya taba yi wa Ingila wasa a kungiyar matasa.

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta bashi damar ya buga wa kasarsa ta haihuwa wasa.

Frimpong zai buga wa Ghana wasa ne a karawar da za ta yi da Sudan ta neman shiga gasar cin Kofin Duniya a watan Maris din nan.

Fatan dan wasan daman shi ne Ghana ta gayyace shi ya yi mata wasa.