Zakarun Afrika: Pillars za ta kara da Leopards

Zakarun Afrika
Image caption Al Ahly ne masu rike da kanbun gasar

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars za ta kara da AFC Leopards na Congo Brazzaville a gasar cin kofin zakarun Afrika, yayin da masu rike da kanbun Al Ahly za su kara da Tusker.

Pillars wacce ta kai wasan kusa da na karshe a karon farko da ta fara halartar gasar, ta fara gasar Premier ta Najeriya ta bana da kafar dama inda ta doke Wikki Tourist da ci 1-0.

Daya kulob din da ke wakiltar Najeriya a gasar Enugu Rangers, za su yi tattaki ne zuwa Vital'O na kasar Burundi.

Ahly za su sanya 'yan wasan da basu kware sosai ba saboda matsalar kudi wacce ta tilasta musu bayar da aron 'yan wasa da dama.

Baya ga haka, wasu 'yan wasan kuma sun samu rauni sannan wasu sun tafi kasashensu domin taka leda.

Jerin wasannin da za a fafata

JSM Béjaïa - Asante Kotoko Tusker FC - Al-Ahly Zanaco FC - Orlando Pirates Chiefs - TP Mazembe Séwé Sport - Al-Hilal Omdurman ASFA Yennega - ES Sétif St. George Addis Abeba - Djoliba AC Bamako Vital'O - Enugu Rangers CRD Libolo - Al-Merreikh Omdurman Kano Pillars - Léopards de Dolisié CA Bizertin - Dynamos AFAD Djékanou - Coton Sport Garoua CD 1º de Agosto - Espérance Tunis