An raba kungiyoyi a gasar Europa

Europa
Image caption Za a fafata wasannin ne a ranakun 4 da kuma 11 ga watan Afrilu

An raba kungiyoyin da za su fafata a wasan daf da na kusa da na karshe (quarter-final) a gasar cin kofin kwallon kafa na Europa.

Duka kulob-kulob uku da suka fito daga Ingila wato Chelsea, Tottenham da Newcastle ba za su hadu da juna ba a wannan matakin.

Chelsea wacce ita ce mai rike da kanbun gasar zakarun Turai, za ta kara ne da Rubin Kazan, yayin da Tottenham za ta fafata da FC Basel.

Lazio na kasar Italiya za su kece raini ne da Fenerbahce.

Za a fafata wasannin ne a ranakun 4 da kuma 11 ga watan Afrilu.

Ga yadda wasannin za su kasance:

Chelsea da Rubin Kazan

Tottenham Hotspur da FC Basel

Fenerbahce da Lazio

Benfica da Newcastle United