Ingila ta sake gayyatar Ferdinand

rio ferdinand
Image caption Rio Ferdinand sau 81 yana buga wa Ingila wasa

Ingila ta sake gayyatar Rio Ferdinand domin buga mata wasan neman zuwa gasar cin Kofin Duniya na kwallon kafa.

Ingila za ta kara ne da San Marino da Montenegro a wasannin neman tsallakewa zuwa gasar Kofin Duniyar.

Dan wasan bayan na Manchester United rabonsa da bugawa Ingila wasa tun a watan Yuni na 2011 da ta yi 2-2 da Switzerland.

Ferdinand mai shekara 34 wanda ya fara buga wa Ingila wasa a 1997 a karawarta da Kamaru sau 81 ya na yi mata wasa.

Kocin Ingila Roy Hodgson ya ce ya dauke shi ne saboda yana wasa da kyau kuma kungiyarsa ita ma tana kokari sosai a yanzu.

Yana mai fatan zai taimaka musu samun nasara a wasannin biyu saboda hakan shi ne mafi amfani a gare su kamar yadda ya ce.

Shi ma mai tsaron gida Ben Foster mai shekara 29 an gayyace shi cikin 'yan wasan Ingilan a karon farko tun bayan da ya bukaci tsohon kocin kasar Fabio Capello da kada ya gayyace shi a watan Mayu na 2011.

A ranar Juma'a 22 ga watan Maris Ingila za ta kara da San Marino kafin ta tafi Montenegro ranar Talata 26 ga watan Maris domin wasan da zai iya tantance kasar da za ta yi nasara a rukunin Group H.

Karin bayani