Rafael Nadal ya doke Roger Federer

Rafael Nadal
Image caption Rafael Nadal na farfadowa bayan raunin da ya yi fama da shi

Rafael Nadal ya doke Roger Federer da ci 6-4 6-2 a ci gaba da farfadowar da yake yi bayan raunin da ya yi fama da shi.

A yanzu ya samu nasarar kaiwa wasan kusa da na karshe a gasar Indian Wells da ake yi a jihar California ta Amurka.

Federer, wanda yayi fama da matsalar ciwon baya a lokacin wasan, ya taka rawar gani da farko kafin Nadal ya yunkuro ya lashe kashin farko.

"Bayan shafe watanni takwas ba a fafata wa da ni, ina murna ganin na zo wasan kusa da na karshe," a cewar Nadal.

A yanzu Rafael Nadal zai hadu da Tomas Berdych a wasan kusa da na karshe.

"Makonni biyu da suka wuce ba ni da tabbas ko zanzo nan, amma yanzu gani a wasan kusa da na karshe. Ina samun kwarin gwiwa sosai".