West Brom za ta ladabtar da Odemwingie

peter odemwingie
Image caption Peter Odemwingie ya biya tarar albashinsa na sati biyu

Kungiyar West Brom ta ce za ta ladabtar da Peter Odemwingie sakamakon sukan klub din da ya yi kwanan nan.

A watan Janairu kungiyar ta hukunta dan wasan mai shekaru 31 bayan kalaman da ya yi a shafin intanet na twitter saboda hana shi damar barin kungiyar.

Odemwingie dan Najeriya ya kuma sake batanci ga kungiyar bayan tafiyar da ya yi ba tare da izini ba ranar karshe ta musayar 'yan wasa a yunkurinsa na komawa QPR yunkurin da ya ci tura.

A ranar Lahadi Odemwingie ya soki kungiyar saboda fitar da shi daga jerin 'yan wasanta 11 na farko dake buga mata wasa akai-akai.

Rabon da a sa shi a farkon wasa tun watan Janairu bayan yunkurin da ya yi na barin klub din.

Daga cikin irin kalaman da dan wasan yake yi na sukan kungiyar a shafin twitter ya ce ''ajiye ni da suke yi a benci yanzu yafi muni a kan abin da suka yi min ranar 31 ga wata (na hana shi barin kungiyar).''

A kan hakan wani mai goyon bayan kungiyar ya maida masa martani ta shafin na twitter da cewa ya kamata a kore shi, shi kuma ya mayar masa da cewa : ''Daman fatana ke nan.''

Bayan kakar wasanni ta bana Odemwingie yana da sauran shekara daya a kungiyar.