An kama magoya bayan West Ham

chelsea da west ham
Image caption Chelsea da West Ham na tsananin hamayya a Landan

An kama magoya bayan West Ham biyu saboda zargin aikata laifin wariyar launin fata a lokacin wasan kungiyarsu da Chelsea a Stamford Bridge ranar Lahadi.

Hukumar 'yan sandan birnin Landan wadda ta sanar da hakan ta ce an bada belin mutanen har zuwa wani lokaci a nan gaba cikin watan nan.

An kama mutanen ne yayin da 'yan sandan kuma suka fara gudanar da wani binciken na dabam a kan jifa da aka yi da kwandaloli cikin fili lokacin da Frank Lampard ya ci kwallonsa ta 200 a wasan da Chelsea ta ci 2-0.

Lokacin da Lampard ya ke murnar cin kwallon da John Terry an ga wasu abubuwa da aka jefe su da su daga wurin 'yan kallo.

'Yan sanda na nazarin hotunan bidiyo na naurorin daukar hoto na filin sai dai kawo yanzu ba a kama wani mutum ba dangane da jifan.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA ta ce za ta hadu da 'yan sanda da kuma kungiyoyin wasan biyu don gudanar da bincike.

Shekaru tara da suka gabata aka jefi Frank Lampard wanda ya koma Chelsea daga West Ham a 2001 da kwandala lokacin karawar kungiyoyin da suke tsananin hamayya da junansu a Landan.

Karin bayani