Damben boksin : an daina sa makarin kai

makarin kai na damben boksin
Image caption Ba a tabbatar ko ba za a sa makarin kai a gasar Olympics ta 2016 ba

Hukumar damben boksin ta wadanda ba kwararru ba ta duniya ta tabbatar cewa za a daina sanya makarin kai a lokacin damben matasan.

Sai dai hukumar tace dokar za ta shafi maza ne kawai mata za su ci gaba da amfani da makarin.

A shekarar 1984 aka bullo da tsarin sanya sosan kariyar a lokacin damben matasa.

Amma kuma yanzu ba za a yi amfani da shi ba a lokacin gasar damben ta duniya ta wadanda ba kwararru a Kazakhstan a watan Oktoba.

Hukumar ta dauki matakin daina amfani da makarin ne bayan nazarin rahotannin wasu bincike biyu da ta yi da suka nuna cewa daina sanya shi zai rage hadarin jin rauni a ka.