Atsu ba zai bugawa Ghana wasa ba

christian atsu
Image caption Likitocin Porto sun ce Christian Atsu ba zai iya wasa ba

Dan wasan Ghana Christian Atsu ya janye daga shirin bugawa kasar wasan neman shiga gasar Kofin Duniya da Sudan saboda rauni.

Dan wasan na tsakiya ya ji rauni ne a idon sawunsa a lokacin da ya ke yi wa kungiyarsa ta FC Porto wasa a karshen makon da ya gabata.

Likitocin sun ce dan wasan ba zai iya yin wasan ba na ranar Lahadi wanda za a yi a Kumasi a filin wasa na Baba Yara.

Yanzu tawagar 'yan wasan da kociyan Ghanan Kwesi Appiah ya zaba mai mutane 24 ta ragu da dan wasa daya.

Ghana ce ta biyu a rukuninsu na hudu, Group D wanda Zambia ke gaba da maki 3, Sudan da Lesotho na bi musu da maki dai-dai.

Karin bayani