Odimwingie ya ce zai saye kwantiraginsa

osaze odimwingie
Image caption Takun sakar Odimwingie da West Brom ya dauki wani salo

Dan wasan kungiyar West Brom dan Najeriya Peter Odimwingie ya ce zai saye kwantiraginsa da klub din domin ya fita daga ciki.

Dambarwar da dan wasan ke yi da kungiyar tasa ta dauki wannan salon ne kuma inda ya rubuta a shafinsa na twitter cewa zai duba yuwuwar hakan.

Yace ''ina ganin dan wasan da babu wani kwantiragi a kansa nan ba da jimawa ba, ko kuma dan wasan da ya yi ritaya.''

Odimwingie ya shiga takun saka ne da West Brom tun bayan da ya yi yunkurin komawa QPR a ranar karshe ta musayar 'yan wasa a Disamba abin da bai samu nasara ba.

Kuma klub din ya daina sa dan wasan wanda ya ke da sauran watanni 15 a kwantiraginsa wasa akai-akai kamar da.

Kafin wadannan kalaman na dan wasan an ruwaito kungiyar ta West Brom tana cewa zata ladabtar da shi a cikin gidanta.