Owen zai yi ritaya daga kwallon kafa

Michael Owen
Image caption Owen ya fara haskakawa ne a wasan Ingila da Argentina a 1998

Tsohon dan wasan Ingila Michael Owen zai yi ritaya daga kwallon kafa a karshen kakar wasanni ta bana.

Owen, mai shekaru 33, wanda ya zira kwallaye 40 a wasanni 89 na kasa da kasa, ya taka leda a Liverpool, Real Madrid, Newcastle United da Manchester United sannan yanzu kuma yana Stoke.

Ya ce: "ina matukar alfahari da sanar da cewa zan yi murabus daga kwallon kafa kwata-kwata.

Na yi matukar dace ganin yadda na samu damar buga kwallo a kungiyoyi daban-daban wadanda ban taba tunani ba".

Owen ya fara shahara ne tun yana matashi a Liverpool sannan ya shiga tawagar Ingila da ta halarci gasar cin kofin duniya a 1998 yana dan shekara 18.

Ya fara fice ne lokacin da ya zira kwallo a wasan da Ingila da buga da Argentina a gasar, sannan ya zira kwallaye uku lokacin da Ingila ta lallasa Jamus da ci 5-1 a birnin Munich a shekara ta 2011.

Karin bayani