Joe Allen ya bar wasa bana

joe allen
Image caption Joe Allen zai yi jiyya har karshen kakar bana

Dan wasan tsakiya na kungiyar Liverpool Joe Allen ba zai samu damar cigaba da buga wasa ba har zuwa karshen kakar wasannin bana.

Hakan ta kasance ne domin za ayi wa dan wasan tiyatar wani ciwo da ya ke damun sa ne a kafadarsa ta hagu ranar Alhamis.

Ciwon ya shafi kwazon dan wasan a kwanakinnan inda har ta kai anyi canjin sa a wasan da Southampton ta yi nasara a kan Liverpool 3-1.

Ana saran Allen zai dawo wasa lokacin da Liverpool za ta je rangadin wasanni a Asia.

Tuni tsohon dan wasan ya janye daga tawagar ‘yan wasan Wales da za ta buga wasan neman shiga gasar Kofin Duniya da Scotland da kuma Crotia.

A shekarun baya an taba yi wa dan wasan na Liverpool tiyata a kan ciwon amma kuma yanzu ya sake dawo masa.