Italiya da Brazil sun tashi 2-2

italy da brazil
Image caption Italiya ce ta biyar Brazil ta goma sha takwas a duniya

Kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Italiya da Brazil sun tashi canjaras 2-2 a wasan sada zumunta da suka yi a birnin Geneva na Switzerland.

Brazil ce ta fara cin kwallayenta biyu tun a farkon lokaci inda a minti na 33 Fred ya jefa ta farko kafin kuma a minti na 42 Oscar ya kara ta biyun.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma Italiya ta rama duka kwallayen biyu.

D. De Rossi ne ya fara ramawa Italiyan kwallon farko a minti na 54.

Minti uku tsakani ne kuma sai Mario Balotelli ya rama ta biyun.

Italiya ce ta biyar a jerin gwanayen kwallon kafa na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ita kuma Brazil ta na matsayi na 18.