Golf : Woods na kan hanyar dawo wa na 1

tiger woods
Image caption Tiger Woods ''burina shi ne na fi yadda nake a da''

Tsohon zakaran wasan Golf na duniya Tiger Woods ya kama hanyar sake zama na daya a gasar Arnold Palmer a Florida.

Woods dan Amurka wanda ke rike da kofin gasar wanda kuma sau 7 yana daukar kofin zai maye gurbin zakaran golf din na duniya na yanzu Rory Mcllroy dan Arewacin Ireland wanda ba ya cikin gasar.

Tsohon zakaran wanda ya dauki kofunan manyan gasanni 14 da kuma ya rike kambun zakaran golf din na duniya tsawon makwanni 623 rabonsa da wannan kambu tun watan Oktoba na 2010.

Ya ce ba wai yana son komawa kan matsayinsa na da ba ne na zakaran duniya kawai yanzu yana son ya dara bajinta da kwarewarsa a wasan na golf fiye da da.

Woods ya samu nasara a gasa hudu da ya shiga a wannan shekarar, inda ya dauki kofin wasan golf na duniya makwanni biyu da suka wuce a Doral bayan nasararsa a gasar Torrey Pines a watan Janairu.

Karin bayani