Lesotho ta yi wa Zambia kancal

lesotho zambia
Image caption Lesotho ta yi wa Zambia kafar ungulu

'Yan wasan kasar Lesotho sun hana tsoffin zakarun kwallon kafa na Afrika Zambia galaba a kansu inda suka tashi 1-1.

Zambia wadda ta yi kusan dukkanin wasan rabin lokaci da 'yan wasa goma saboda alkalin wasa ya kori mai tsaron gidanta suna gaba ne da ci 1 amma a minti na 89 Lesotho ta rama.

Saura minti 17 ne a tashi daga wasan Collins Mbesuma ya jefa wa Zambia kwallonta kafin Litsepe Marabe ya rama ana saura minti daya lokaci ya cika.

Sakamakon ya haifar da koma baya ga fatan Zambia na fitowa daga rukuninsu na 4 (Group D) kuma ya kara karfafa wa Ghana gwiwa wadda ita kuma ta samu nasara a kan Sudan 4-0.

Can a Addis Ababa Habasha (Ethiopia) na gab da samun damar zuwa gasar Kofin Duniya a karon farko bayan da ta samu nasara a kan Botswana 1-0.

Da nasarar Habasha ta zama ta daya a rukuni na 1 (Group A) da maki 7 bayan da G. Kebede ya ci kwallo daya ta karawar a minti na 88.

Karin bayani