Kociyan Barcelona zai koma Spain

tito vilanova
Image caption Tito Vilanova ya gaji Guardiola a 2012

Kociyan Barcelona Tito Vilanova zai koma Spain a wannan makon bayan maganin cutar daji da aka yi masa a New York.

An yi wa Vilanova mai sekaru 44 tiyata aka cire masa wani kurji a makogaronsa a watan Nuwamba na 2011 kafin wani kurjin ya sake fito masa.

A watan Disamba na 2012 aka sake yi wa Vilanova tiyata kuma ya na Amurka tun 21 ga watan Janairu domin ci gaba da jiyya.

Sai dai kuma Barcelona ba ta tabbatar da lokacin da kociyan zai koma bakin aikinsa ba gadan-gadan.

Barcelona ta yi wasanni 13 ba tare da Vilanova ba kuma ta sami nasara a 8 ta yi rashin nasara a 3 daga ciki.

A lokacin da baya nan Real Madrid ta fitar da Barcelonan daga gasar Kofin Kalubale na kasar na Copa del Rey a wasan kusa da na karshe.

Sai dai kuma duk da kociyan baya nan Barcelonan ta ci gaba da zama ta daya da maki 13 a gasar La Liga ta kuma fitar da AC Milan daga gasar Zakarun Turai da ci 4-0 bayan a karawar farko Milan din ta yi nasara a kanta da ci 2-0 a Italiya.

Karin bayani