Brazil da Rasha sun tashi 1-1

luiz felipe scolari
Image caption Scolari har yanzu ya na neman nasara a karo na biyu na kociyan BRazil

Brazil da Rasha sun tashi 1-1 a wasan sada zumunta a filin Stamford Bridge na kungiyar Chelsea da ke Landan.

A kashin farko na wasan ba bu kasar da ta ci kwallo, amma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 73 Viktor Faizulin ya ci wa Rasha kwallonta.

Can a minti na 90 ana shirin tashi daga wasan Frederico Chaves ya rama wa Brazil kwallon.

Har yanzu Brazil ba ta yi nasara a wani wasanta ba a karkashin kociyanta Luiz Felipe Scolari wanda ke rike wannan matsayi a karo na biyu.

Yayin da shi kuwa kociyan Rasha Fabio Capello wasansa na 8 ke nan ba ayi galaba a kan Rasha ba.

A wasan sada zumuntar da aka yi kuwa tsakanin Canada da Belarus a Doha Belarus ta yi nasara da 2-0.