Matan Arsenal na taka rawar gani

Matan Arsenal na taka rawar gani
Image caption Matan Arsenal dai na kokarin yin abinda mazansu suka gaza

Tawagar mata ta Arsenal ta kai zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai bayan da suka doke ASD Torres da ci 1-0 wato 4-1 a wasa gida da waje.

Wannan ne karo na uku ajere da matan Arsenal din ke kaiwa wannan mataki.

Niamh Fahey ce ta zira kwallo dayan da suka zira a minti hudu da fara wasan.

Silvia Fuselli, da Giulia Domenichetti da Sandy Iannella duka sun kai munanan hare-hare daga bangaren Torres, wadanda ke kokarin zuwa wasan kusa da na karshen a karon farko.

Sai dai mai tsaron gida ta Arsenal Emma Byrne ta yi kokari sosai wurin hana kwallaye da dama shiga raga.

Arsenal sun lashe wasan farko da ci 3-1 abinda ya basu kwarin gwiwa a karawar ta filin wasa na Vanni Sanna a Sardinia.