Har yanzu Chelsea na raina - Mourinho

Jose Mourinho
Image caption Mourinho ya rike Porto da Chelsea da Inter kafin ya koma Madrid

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya kara ruruta rahotannin da ke alakanta shi da koma Chelsea inda ya ce kulob din "na nan a ransa" kuma wata rana zai koma Ingila.

A makon da ya gabata an ta rudani kan makomar Mourinho inda wasu rahotanni ke cewa tsohon kocin na Porto, da Chelsea da Inter zai koma Stamford Bridge.

Yanzu kocin ya bayyana irin "babbar alakar da ke tsakaninsa" da Chelsea, alakar da ke nuna cewa wata rana "zai koma Ingila, ko ma Chelsea."

"Ba zan iya karyata wannan ba, ina sha'awar zama a nan, ina da gida kuma ina da alaka da Chelsea," kamar yadda ya shaida wa Sky Sports News.

Ganin kalamansa na baya-bayan nan, da yawa za su yi zaton cewa yana kan hanyarsa ta komawa Chelsea ko Ingila ne.

Sai dai Jose Mourinho ya nace cewa a yanzu yana mayar da hankalinsa ne kawai kan Real Madrid.

Karin bayani