Kofin Duniya : Masar ta ci Zimbabwe

tawagar 'yan wasan masar
Image caption Masar na kan hanyar zuwa gasar Kofin Duniya

Masar ta ci Zimbabwe 2-1 a wasan neman zuwa gasar Kofin Duniya bayan da Mohamed Aboutrika ya ci wani bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Minti biyu kafin a tashi daga wasan tsohon dan wasan bayan na Masar ya ci fanaretin bayan an kayar da Mohamed Salah a wasan da aka yi a birnin Askandriya na Masar.

Masar din ce ta fara cin kwallo ta hannun Hosny Abd Rabou amma kuma Zimbabwe ta rama lokacin da dan wasanta Knowledge Musona ya sheko wata kwallo daga nesa.

Da wannan nasara Masar ce ta daya a rukuni na 7 (Group G), da maki 9 wato maki 4 ke nan tsakaninta da ta biyu Guinea.

'Yan kallo 10,000 ne aka bari suka kalli wasan bayan da ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta yadda a kyale kayyadaddun 'yan kallo su shiga filin wasa a kasar.

Wanda shi ne karon farko tun hargitsin filin wasan Port Said a watan Fabrairu na 2012 da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 70.

Masar na dab da samun damar zuwa gasar Kofin Duniyar bayan da ta ci Mozambique ta kuma bi Guinea gida ita ma ta yi galaba a kanta a watan Yuni.

Wannan shi ne karon farko da Masar zata je gasar Kofin Duniya tun 1990.

Zimbabwe wadda Guinea ta ci ta a gida kuma ta yi canjaras da Mozambique ita ce ta karshe a rukunin.

A rukuni na 8 kuwa Group H Algeria ta zama ta daya bayan da ta yi nasara da ci 2-1 a kan Jamhuriyar Benin a wasan da aka yi a Algeria.

Da nasarar Algerian ta karbe ragamar jagorancin rukunin daga hannun Mali.