Zan iya kare rayuwata a United - RVP

 Robin van Persie
Image caption Robin van Persie yana taka rawa sosai a Man United

Robin van Persie ya ce mai yiwu wa ya kasance a Manchester United har karshen rayuwarsa ta kwallo.

Dan wasan na kasar Netherlands, mai shekaru 29, ya koma United ne daga Arsenal kan kudi fan miliyan 24 a watan Agustan bara, inda ya sanya kwantiragin shekaru hudu.

Shi ne dan wasa na biyu wurin zira kwallaye a gasar Premier ta bana bayan Luis Suarez.

Sai dai kwallaye 19 da ya zira sun taimaka wa United ta bayar da tazarar maki 15 a saman teburin Premier a yayin da ya rage wasanni takwas a kammala kakar ta bana.

"Nan da 'yan shekaru masu zuwa zan ci gaba da zama a United - ko ma fiye da haka," a cewar Van Persie. "Ba mamaki United ta zamo kulob di na na karshe."

Van Persie ya zira kwallaye 37 a kakar wasanni ta karshe da ya buga a Arsenal.

Kuma masu sharhi na ganin rawar da yake taka wa a United ta taimaka wa kulob din kan nasarar da yake samu a gasar Premier ta bana.

Karin bayani