Southampton ta doke Chelsea da ci 2-1

Southampton
Image caption A yanzu Southampton ta koma mataki na 13 a teburin gasar Premier

Fatan Chelsea na shiga gasar zakarun Turai ya fuskanci koma-baya bayan da suka sha kashi a hannun Southampton da 2-1 a gasar Premier ta Ingila.

Jay Rodriguez ne ya fara zira kwallo a ragar Chelsea a minti na 23 da fara wasa bayan kyakkyawar ledar da Lambert da Steven Davis suka taka.

John Terry ya rama wa Chelsea a minti na 33 a wasan farko da aka fara da shi a gasar Premier tun ranar 2 ga watan watan Fabreru.

Sai dai kwallon da Lambert ya zira a bugun tazara daga yadi na 25 ya nuna cewa Chelsea ta sha kashi a karo na uku a jere a wasannin da ta buga a waje na League.

A yanzu Southampton ta koma mataki na 13 a teburin gasar Premier bayan da 'yan wasan na Mauricio Pochettino suka lashe wasa biyu a jere a karon farko tun watan Nuwamba.

Ga yadda wasannin wannan makon suka kaya:

Sunderland 0 - 1 Manchester United Arsenal 4 - 1 Reading Manchester City 4 - 0 Newcastle United Southampton 2 - 1 Chelsea Swansea City 1 - 2 Tottenham Hotspur West Ham United 3 - 1 West Bromwich Wigan Athletic 1 - 0 Norwich City