Fulham ta kara jefa QPR tsaka mai wuya

fulham da qpr
Image caption Fulham ta lallasa QPR

Kungiyar QPR ta sake shiga cikin hadarin faduwa daga gasar Premier bayan da Fulham ta yi galaba a kanta da ci 3-2.

Berbatov ne ya ci wa Fulham kwallayenta 2 kafin daga bisani Hill ya ci kansu da kansu suka zama 3-0.

Adel Taarabt shi ne ya farfadowa QPR kwarin guiwarta kafin a tafi hutun rabin lokaci da kwallo ta farko.

Loic Remy shi ma ya sake rama kwallo ta biyu bayan ya zubar da bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida.

Duk da korar Steve Sidwell na Fulham da alkalin wasa ya yi QPR ba ta iya rama kwallon ba su ka tashi 3-2.