Zan yi wa Ingila wasa - Beckam

david beckam
Image caption David Beckam ya koma PSG a watan Janairu

Tsohon kyaftin din kwallon kafa na Ingila David Beckam ya ce har yanzu bai fitar da tsammanin sake bugawa Ingila wasa ba.

Dan wasan na kungiyar Paris St-German ta Faransa ya ce ''yanzu na kusa cika shekaru 38 da haihuwa a don haka damar kadan ce amma kuma ba za ka fitar da tsammani ba.''

Beckam shi ne dan wasan da ya fi bugawa Ingila wasa wanda sau 115 ya na shiga wasanninta amma rabon da a sa shi tun watan Oktoba na 2009.

Ya ce daya daga cikin dalilan da suka sa bai yi ritaya daga kungiyar wasan Ingila ba shi ne idan ya samu damar sake yi wa kasar wasa to a shirye yake.

Tsohon dan wasan na Manchester United da Real Madrid wanda ya koma kungiyar PSG a kan saka shi a matsayin canji a wasannin kungiyar ta Faransa.

Amma duk da haka klub din ya ce zai cigaba da rike shi har bayan kwantiraginsa na yanzu.

Shugaban klub din na PSG Nasser Al-Khelaifi ya ce ''Beckam a matsayinsa na mutum, dan wasa, jakada, dan baiwa ne.''