Fifa ta bada umarnin samar da na'urar tantance cin kwallo

dambarwar shigar kwallo raga
Image caption Za a yi amfani da na'urar a gasar zakarun nahiyoyi

Hukumar kwallon kata ta duniya Fifa ta zabi kamfanin Jamus GoalControl domin ya samar da na'urar tantance shigar kwallo raga a gasar Kofin Duniya ta 2014 da za a yi a Brazil.

Za a fara amfani da na'urar ne a gasar Kofin Zakarun Nahiyoyi da za a yi a bana a Brazil din sannan kuma a cigaba da amfani da ita a shekara mai zuwa idan an gamsu da ita.

Fasahar ta kunshi na'urorin daukar hoto ne guda 14 da za a kafa a can sama a filin wasa, kowace raga ta na da 7 da aka saita kanta da zasu rika daukar hoton motshin kwallon.

Da zarar kwallon ta tsallaka layin bakin ragar na'urar da ta ke tattara ayyukan kyamarorin daukar hoton za ta aika wa alkalin wasa bayani na murya cewa kwallon ta tsallaka layi wato ta ci ta agogonsa.

Kuma duka wadannan abubuwa za su kasance ne cikin dan kankanin lokacin da ya ke kasa da dakika daya.

Shugaban Fifa Sepp Blatter ne ya matsa da a bullo da wata fasaha da za arika amfani da ita domin tantance shigar kwallo raga tun bayan da alaklin wasa ya hana kwallon da Frank Lampard ya ci a karawar da Jamus ta lallasa Ingila 4-1 a gasar Kofin Duniya ta 2010.

Hukumar kwallon kafa da hukumar gasar Premier ta Ingila suna tattaunawa da kamfanonin samar da fasahar kan yadda za su samar da na'urar a dukkanin filayen wasan Premier 20.

Kuma ana ganin za su cimma yarjejeniya a farkon watan nan kan kamfanin da za a baiwa kwangilar samar da na'urorin.