Conte - Ba ma jin tsoron Bayern Munich

antonio conte
Image caption Antonio Conte yana son Juventus ta mamaye gasar Zakarun Turai

Kociyan Juventus Antonio Conte ya ce kungiyarsa za ta fuskanci Bayern Munich ba tare da wata fargaba ba.

Kociyan yana magana ne kafin karawarsu ta farko ta wasan dab da na kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai ranar Talatar nan.

Bayern ta lallasa Hamburg 9-2 a wasan lig din Jamus ranar Asabar kuma ta na bukatar maki biyu ne kawai a wasanninta 7 da suka rage ta dauki Kofin lig din na Bundesliga.

Amma duk da haka Conte ya ce su basu da wata damuwa ko fargaba a kan haka za su Munich ba tare da tsoro ba kuma da kwarin guiwa.

Ya ce ''mun san cewa zamu hadu ne da kungiyar Bayern da take da karfi amma muna da kyakkyawan fata.''

Su ma 'yan Juventus zakarun Italiyan ba kanwar lasa ba ne domin a karshen mako sun cigaba da rike tazarar maki taransu ta lig din kasar a kan Napoli bayan da suka ci Inter Milan 2-1.

Shi ma kociyan Bayern Munich Jupp Heynkes ya ce ba ya tsammanin za su maimaita irin abin da suka yi wa Hamburg idan suka hadu da Juventus.

Ya ce Juventus tana daya daga cikin manyan kungiyoyin Turai.