Chelsea na ran Mourinho - Drogba

drogba mourinho
Image caption Didier Drogba ya ce '' ina ganin zai fi dacewa Chelsea ta dawo da Mourinho''

Didier Drogba ya ce Mourinho ka iya komawa Chelsea saboda yana ganin bai cika burinsa ba a kungiyar.

Dan wasan na daga cikin wadanda kociyan yafi sawa a wasa a kai akai a shekaru uku da ya yi a klub din.

Drogba yana daga cikin 'yan wasan Galatasaray da zasu kara da Real Madrid ta Mourinho ranar Larabar nan, a gasar Kofin Zakarun Turai wanda Drogba ya dauka da Chelsea.

Drogba wanda ya bar Chelsea a karshen kakar wasannin da ta gabata ya ce yana ganin tsohon klub din nasa zai amfana da Mourinho mai shekara 50 a kaka mai zuwa.

Ya ce rashin daukar Kofin Zakarun Turai da Chelsea ka iya sa Mouriho ya so dawowa kungiyar domin cimma wannan buri.

Shi kansa Drogba na iya dawowa Chelsea idan mai kungiyar Roman Abramovich ya dawo da Mourinho.

Sai dai tsohon dan wasan na Marseille wanda Mourinho ya kawo Chelsea a 2004 game da hakan cewa ya yi, '' bari in gama da Galatasaray tukuna sannan mu yi magana a kan hakan.''

Amma ya kara da cewa har yanzu yana sha'awar Chelsea.

Karin bayani