Yaya Toure ya sabunta kwantiragi

yaya toure
Image caption Yaya Toure zai cigaba da zama a Man City har 2017

Dan wasan tsakiya na Manchester City Yaya Toure ya kulla sabon kwantiragi na shekaru 4 da kungiyar.

Dan wasan dan kasar Ivory Coast yanzu zai cigaba da zama a klub din har zuwa shekara ta 2017.

Rahotanni sun ce kwantiragin nasa ya kai kusan dala miliyan 70.

A da dai ana ta rade-radi game da cigaba da kasancewarsa a kungiyar.

A 2010 ne Man City ta sayo dan wasan daga Barcelona a kan fam miliyan 24, bayan ya taimakawa kungiyar ta Spaniya wajen daukar kofin Zakarun Turai a 2009.