Sakamakon Premier

qpr wigan
Image caption QPR na tsaka mai wuya a Premier

A ranar Lahadin nan aka cigaba da gasar Premier inda aka yi wasanni biyar.

Liverpool 0-0 West Ham

Tottenham 2-2 Everton

New Castle 1-0 Fulham

QPR 1-1 Wigan

Chelsea 2-1 Sunderland

Sakamakon wasan Liverpool ya sa burinta na shiga Gasar Zakarun Turai na badi ya shiga tsaka mai wuya yayin da West Ham ta kara nisa da hadarin faduwa daga Premier.

Ita kuwa Newcastle nasarar da ta samu a kan Fulham ta sa ta tsira da maki biyar daga hadarin faduwa daga Premier.

Wigan ta na cikin rukunin ficewa daga gasar ta Premier da bambancin kwallaye ne kawai amma ba maki ba yayin da QPR ta ke cikin hadari saboda kungiya daya kawai ta wuce da maki 24 ragowar wasanni 6.